11-Aug-2026
10-Aug-2026
09-Aug-2026
07-Aug-2026
06-Aug-2026
20260811-Yamai
00:00
1x
Shirin Duniyarmu A Yau na wannan karo ya dau harama ne daga wani tsohon karin magana na Sinanci da yake cewa, “Shin ba abin farin ciki ba ne a sami abokai suna zuwa ziyararka daga nesa?” Wannan kyakkyawar magana tana nuna farin cikin karbar baki, da gina amincewa, da karfafa dangantaka. Sannan, baya ga abota tsakanin mutane, hikimar wannan karin magana tana kuma bayyana yadda kasashe ke hulda da juna ta hanyar diflomasiyya, da tattaunawa da kuma kulla hadin gwiwa domin samun ci gaba.
“Na zo Chengdu don ganin manyan dabbobin Panda, kuma sai na zauna saboda mutanen birnin da kuma harkokin wasanni,” cewar Lamia Arab wadda ta zo Sin daga birnin London na Birtaniya. Ta je Chengdu, babban birnin lardin Sichuan ne a 2017. Yanzu malama ce a jami’ar Chengdu. Wasanni sun zama tamkar fasfonta yayin zama a Chengdu, al’ada kuma ta zama abun da ya zaunar da ita a birnin. A ganinta, Chengdu ba waje ne mai hada-hada ba kadai, misali ne na wurin da ya hada wasanni da al’adu, kuma inda gargajiya da zamani suka hade da juna.
04-Aug-2026
28-Jul-2026
08-Aug-2026